- WOULD
Would itama kalma ce da ake amfani da ita don neman izini ko wata bukata a turance kamar sauran yan'uwanta. Sai dai sau tari akan yi amfani da kalmar don bawa wanda ka/ki ke magana da shi cikakkiyar girmamawa. Haka kuma, kalmar Would a
sau tari akan yi amfani da ita tare da kalmar "Please" don nuna cikakkayar girmamawa don neman biyan bukata a take. Misali: Would you please assist me? (Zan iya samun taimakon ka/ki kuwa?)
Ga misalai da kalmar Would kamar haka:
- Would you please wait for me? (za ka/ki iya jirana kuwa?)
- Would you please read it for me ? (za ka/ki iya karantamun shi (abun/rubutun) kuwa?)
- Would you give this letter to her? (za ka/ki iya bata wasika/sako na kuwa?)
- Would you please hold it for me? (za ka/ki iya rike min kuwa?)
- Would I take tomorrow off ? (za iya daukar hutu gobe?)
- Would I stay here for two days? (zan iya zama anan na tsahon kwana biyu)
- Would I use your laptop? (zan iya amfani da komfiyutar ka ta tafi da gidanka?)
- Would I see this book please? (zan iya ganin littafin nan kuwa?)
- Would you please repeat it please? (za ka/ki iya maimaitawa kuwa?)
- Would you keep the money for me? (za ka/ki iya ajiye min kudin?)
No comments:
Post a Comment