🛑 ''PHRASAL VERBS''
Gabatarwa (Introduction)
''Phrasal Verbs'' wani jigo ne a harshen Turanci domin suna ɗaya daga cikin abubuwan da dole mutum ya sansu domin iyawa da kwarewa a cikin harshen Turanci. Domin ina muka dauki harshen Turanci gaba ɗaya, muna iya rabashi kaso kamar;
❇️ GRAMMAR - Sannin dokiki da ƙa'idodin harshen Turanci.
❇️VOCABULARY - Sanin kalmomin Turanci.
❇️ IDIOMS - Sanin salon magana na harshen Turanci
❇️ PHRASAL VERBS - Sanin tasarrafin harshen Turanci.
❇️ LITERATURE - Sanin adabi na Turanci.
Idan mukayi duba zamuga mun kasa manyan ɓangarori na gaba ɗaya harshen Turanci guda biyar (5) wanda ɗaya daga cikinsu shine ''Phrasal Verbs'' wato ilimi akan sani na tasarrafin harshen Turanci, kuma ya kasance jigone babba da idan har kana buƙatar ka iya kuma ka kware a harshen Turanci dole ne kasan da yawa daga ''Phrasal Verbs''.
Misali; mu ɗauki wannan ƙunshin kalmomi ''abide by'' wanda ɗaya ne daga cikin phrasl verbs da muke dasu zamuga kalmomi biyune suka taru suka haɗa su, wato kalmar (abide) da kuma kalmar (by) wanda ita kalmar ''abide'' ta kasance ɗaya daga cikin jinsi ne na aikatau wato (verb) wato wannan ya shafi ɓangaren grammar a Turanci, sai kuma ɗaya kalmar ta ''by'' wadda ta kasance ɗaya daga cikin wasu jinsi a fannin ilimin grammar da ake kira da (preposition) to anan zamuga cewa ginshiƙin PHRASAL VERBS ansamo sune daga cikin GRAMMAR sai dai suma suna cin gashin kansu kamar sauran ginshiƙai na Turanci. Sannan kuma zamuga cewa abu biyu ne yawanci suke haɗuwa waje guda su haɗa ''PHRASAL VERBS'' wannan ba komai bane face (Preposition + Verb) shi yasa ma akayi la'akari da furucin su aka kirasu da ''PHRASAL VERBS''.
''Phrasal Verb'' guntuwar jumla ce Mara cikakkiyar ma'ana da ake dunkule su a kirasu da ''phrase'' don haka gaba ɗaya PHRASAL VERBS da ake dasu basa bada cikakkiyar ma'ana su kaɗai dole sai an haɗasu da wasu kalmomin sun bada doguwar jumla mai ma'ana. Misali, wannan phrasal verb na ''abide by'' baya bada cikakkiyar ma'ana dole sai anyi amfani dasu a cikin jumla (sentence) wanda zamu dubasu a darasin mu na gaba.
PHRASAL VERBS na da matuƙar yawa da gaske amma inshaAllah zamuyi duba akan mafi yawa daga cikinsu, duba na tsakanaki domin a sansu kuma a iya amfani dasu a Turanci saboda muhimmacin da suke a Turanci wanda zan ƙara jaddadawa cewa idan har baka sansu ba to fa sai nayi maka rantsuwa wallahi baka iya Turanci ba. Ku biyo mu domin muyi karatu akansu na tsakanaki.
🔰Muna so Don Allah idan har kazo karshe a karatun nan kuyi:
📌 Share
📌 Like
Sannan idan kunada da tambaya ko ƙarin bayani, mu haɗu a comment section.
Director (TALAMIZ ENGLISH)✍️
No comments:
Post a Comment