Anan zamuyi dubane ga gajeriyar jumla ta “HOW DARE YOU” a cikin zance na yau da kullum.
A kan fadi gajeriyar jumlar ne a lokacin da mutum yake cikin fushi a sakamakon abin da wani ya aikata wanda bai dace ba, ko shi bai isa ya aikata hakan ba.
Mukan fassara gajeriyar jumla ta “how dare you” da kai ka isa, kai waye, har ka kai, kai a su wa, da dai sauran su.
Ga misalan yacce ake amfani da ita:
1. How dare you you abuse me (Kai ka isa ka zage ni)
2. How dare you come here (Har ka kai ka zo nan)
3. How dare you shout at me (Har ka isa ka yi min tsawa)
4. How dare you slap him (kai a su wa ka mare shi)
5. How dare beat me (kai a su wa ka dake ni)
Domin koyon turanci cikin sauki a hausance cikin tsari mai kyau a duk inda kuke a duniya ku tuntube mu a +2348065586555
No comments:
Post a Comment