Mukanyi amfani da kalmomin CAN, MAY da MIGHT wajen nuni ga abin da zai iya wakana.
- CAN da MAY sukan fayyace abin da tabbas zai iya wakana, ma'ana abin da munada tabbacin faruwarsa.
- MIGHT a daya hannun akanyi amfani da ita don nuni ga abin da babu tabbacin faruwarsa, ma'ana abin da yake kila wakala.
Ga misalan da suke dauke dasu kamar haka:
1. I can go around 10 o'clock (Zan iya tafiya wajen karfe goma)
2. He can come at anytime (Zai iya zuwa a kowanne lokaci)
3. She can finish today (Zata iya gamawa a yau)
4. They can be at the wedding ceremony (Zasu iya zuwa wajen bikin)
5. We can go home tomorrow (Zamu iya tafiya gida gobe)
6. I may pay the money (Zan iya biyan kudin)
7. He may buy the ticket (Zai iya siyan tikitin)
8. She may cook for us (Zata iya yi mana girki)
9. They may finish the work (zasu iya kammala aikin)
10. We may leave before them (Zamu iya tafiya kafin su)
11. I might go for shopping (Nakan iya tafiya siyayya)
12. He might assist us (Yakan iya taimakon mu)
13. She might be happy to see us (Takan iya yin farincikin ganin mu)
14. They might be in the class now (Sukan iya kasancewa a aji yanzu)
15. We might attend the meeting (Mukan iya halartar taron)
Domin koyon turanci cikin sauki a hausance cikin tsari mai kyau a duk inda kuke a duniya ku tuntube mu a +2348065586555
Domin koyon turanci cikin sauki a hausance cikin tsari mai kyau a duk inda kuke a duniya ku tuntube mu a +2348065586555
No comments:
Post a Comment