A yanayin da mutum zai yi magana akan yacce yake jin kansa a ciki, yana iya amfani da gajeriyar jumla ta I AM FEELING...(Ma'ana ina jin..) sai ya fadi yanayin da yake ji kamar yanayin farinciki, bakinciki, jin dadi, bacci, yunwa, ishinruwa da sauransu. Amma a yanayin da mutum zai fasalta yacce ya sami waje ko wani abu da ya aikata ko yake aikatawa anan zai yi amfani da gajeriyar jumla ta I FOUND...(Ma'ana na sami..)
Ga misalan yacce ake amfani dasu:
1. I am feeling good (Ina jin yanayin dadi)
2. I am feeling bad (Ina jin yanayin damuwa)
3. I am feeling better (Ina jin yanayin damadama)
4. I am feeling hungry (Ina jin yanayin yunwa)
5. I am feeling thirst (Ina jin yanayin ishinruwa)
6. I found him interesting (Na same shi da yanayi na kayatarwa)
7. I found the job boring (Na sami aikin babu kayatarwa)
8. I found the school very nice (Na sami makarantar a yanayi mai kyau)
9. I found him so caring (Na same shi da yanayin kulawa)
10. I found the journey interesting (Na sami tafiyar da yanayi na kayatarwa)
- Domin koyon turanci cikin sauki a hausance cikin tsarin mu na Online (WhatsApp) a duk inda kuke a duniya ku tuntube mu a +2348065586555
No comments:
Post a Comment