Esay and Fastest Way to Learn

Esay and Fastest Way to Learn
Koyon turanci cikin sauki

Saturday, 16 February 2019

“ABOUT TO..” IN USED (Yadda mutum zai yi amfani da “About to” a magana ta Turanci)

Anan zamuyi dubane ga yacce mutum zai yi amfani da gajeriyar jumla ta ABOUT TO a turance.
       Akanyi amfani da ita wajen magana akan abin da lokacin aikata shi ya kusa ko kuma abin da lokacin kammalashi ya kusa. Ma'ana abin da aka kusa farawa ko aka kusa gamawa.
  
         Ga misalai kamar haka:
(A) Abin da lokacin aikata shi ya kusa
1. I'm about to go home (Na kusa tafiya gida)
2. I'm about to start cooking (Na kusa fara girki)
3. I'm about to come in (Na kusa shigowa ciki)
4. I'm about to buy a car (Na kusa siyan mota)
5. I'm about to get ready (Na kusa shiryawa)
6. He is about to go to the market (Ya kusa tafiya kasuwa)
7. She is about to wash the clothes (Ta kusa ta wanke kayan)
8. Fatima is about to go to school (Fatima ta kusa tafiya makaranta)
9. We are about to start exam (Mun kusa fara jarrabawa)
10. They about to come (Sun kusa zuwa)

(A) Abin da lokacin kammalashi ya kusa 
1. I'm about to finish (Na kusa gamawa)
2. I'm about to complete my work (Na kusa kammala aiki na)
3. I'm about to reach market (Na kusa isa kasuwa)
4. I'm about to leave the office (Na kusa barin office)
5. I'm about to finish cooking (Na kusa kammala girkin)
6. He about to come back (Ya kusa dawo wa)
7. She is about to finish her exam (Ta kusa kammala jarrabawar ta)
8. Khadija is about to complete her studies (Khadija ta kusa kammala karatun ta)
9. We are about to leave (Mun kusa tafiya)
10 They are about to finish it (Sun kusa gamawa)


Domin koyon turanci cikin sauki a hausance cikin tsarin mu na Online (WhatsApp) a duk inda kuke a duniya ku tuntube mu a +2348065586555

No comments:

Post a Comment