Esay and Fastest Way to Learn

Esay and Fastest Way to Learn
Koyon turanci cikin sauki

Thursday, 31 January 2019

MAKING FORMAL REQUEST AND PERMISSION (Use of Could/Amfani da Could don neman biyan bukata ko kuma izini)

  •  Could
Hanya ta Uku da ake amfani da ita wajen neman biyan bukata ko kuma izini ita ce hanyar
amfani da kalmar Could. Ana amfani da ita ne sosai a hukumance ko wajen magana da wanda ya girme ka/ki. Amfi so ayi amfani da ita don nuna cikakkiyar girmamawa ga wanda ake magana da shi.
  
        Ga misalan inda zakuyi amfani da ita kamar haka:
  1. Could I make a call? (shin wai zan iya yin kira?)
  2. Could you please open the door? (shin wai za ka/ki iya bude kofar?)
  3. Could you turn down the music? (shin wai za ka/ki iya rage sautin kidan?)
  4. Could you tell me what time it is? (shin wai za ka/ki iya gayamin lokaci?)
  5. Could I take one? (shin wai zan iya daukar guda/daya?)
  6. Could I ask a question? (shin wai zan iya tambaya?)
  7. Could we go home now? (shin wai zamu iya tafiya gida yanzu?)
  8. Could you take the message please? (shin wai za ka/ki iya karbar sakon?)
  9. Could you carry this for me? (shin wai za ka/ki iya daukar min wannan[abu]?)
  10. Could I pay the money for the goods? (shin wai zan iya biyan kudin kayan?)

No comments:

Post a Comment