Esay and Fastest Way to Learn

Esay and Fastest Way to Learn
Koyon turanci cikin sauki

Thursday, 14 February 2019

USE OF "HOW LONG..." IN A SENTENCE (Amfani da "how long.. " a cikin jumla)

Anan zamuyi dubane ga yacce mutum zai yi amfani da "HOW LONG...(Tsahon yaushe...)" a jumlace, saboda muhimmancin ta a yanayin zamantakewa na yau da kullum.
        Mukanyi amfani da "HOW LONG..." a kowanne yanayi da muke dasu wato yanayi da muke a yanzu (Present) ,  yanayin da ya wuce (Past) da kuma yanayin da zai zo (Future). Sai dai a kowanne yanayi a gaban How long dole mu saka TAKE TO

A yanayin da yake gudana a yanzu (Present)

      A nan mukan kara kalmar "Do" ko "Does" ko kuma "Can" a inda ya dace ayi amfani dasu tare da How long don tambaya ga abin da yake gudana a yanzu.
          
         Ga misalai kamar haka:
1. How long do you take to finish the work?
   (Tsahon wanna lokaci zai yi ka gama aikin nan?)

2. How long does he take to reach Lagos?

   (Tsahon wanna lokaci zai dauka ya isa Lagos?)

3. How long does she take to cook the food?

   (Tsahon wanna lokaci zata dauka tayi girkin?)

4. How long can we take to stay here? 

   (Tsahon wanna lokaci zamu dauka anan?)

5. How long can they take to finish the exam?

    (Tsahon wanna lokaci zasu dauka su yi jarrabawar?)


A yanayi na abin da ya wuce (Past)

      Ana mukanyi amfani da kalmar "DID" a gaban "HOW LONG" domin tambaya ga abin da ya gudana a baya.
         
         Ga misalai kamar haka:
1. How long did you take to finish the work?
   (Tsahon wanna lokaci ka dauka wajen kammala aikin?)

2. How long did he take to wash the clothes?

    (Tsahon wanna lokaci ya dauka wajen wanke kayan)

3. How long did she take to cook the food?

   (Tsahon wanna lokaci ta dauka wajen girkin)

4. How long did we take to complete the task?

   (Tsahon wanna lokaci muka dauka wajen kammala aikin)

5. How long did they take to finish the exam?

   (Tsahon wanna lokaci suka dauka wajen zana jarrabawar?)

A yanayi na aikin da za'a aikata nan gaba

        A wannan bangaren mukanyi amfani da kalmar WILL a gaban How long don tambaya akan tsahon lokacin da za'a dauka don aikata wani abin. 

       Ga misalai kamar haka:

1. How long will you take write the exam? 
    (Tsahon wanna lokaci zaka dauka kayi jarrabawar?)

2. How long will he take to repair the car?

    (Tsahon wanna lokaci zai dauka ya gyara motar?)

3. How long will she take to cook the food?

    (Tsahon wanna lokaci zata dauka tayi girkin)

4. How long will we take to finish the work?

    (Tsahon wanna lokaci zamu dauka mu kammala aikin?)

5. How long will they take to make the dress?

    (Tsahon wanna lokaci zasu dauka su dinka kayan)

DOMIN YIN REGISTER DAMU DON SHIGA TSARIN MU NA KOYAR DAKU HARSHEN TURANCI A HAUSANCE A TSARIN MU NA ONLINE A DUK INDA KUKE, KU NEME MU A +2348065586555

5 comments: