Anan zamuyi dubane ga yacce mutum zai yi amfani da gajeriyar jumla ta “GET RID OF” a Turance.
Ana amfani da “get rid of” (wato: kawar da, gusar da, rabu da, ko tsai da) wajen nuni ga abin da mutum ya ga ya dace ya rabu dashi ko sun dace su rabu dashi ko ya daina ko su daina ko ya daina yin sa. Akan yi amfani da ita wajen kore abin da bashi da amfani don a daina aikatashi.
Ga misalan yacce zamuyi amfani da ita:
1. You must get rid of him (Dole ka/ki rabu dashi)
2. You have to get rid of this stuff (Ya kamata ka/ki kawarda abubuwan nan)
3. You have to get rid of smoking (Ya kamata ka/ki rabu da shaye shaye)
4. I have to get rid of the waste (Ya kamata ta kawadda sharar)
5. I want to get rid of my sofa (Ina so na kawadda doguwar kujera ta)
6. They want to get rid of pollution (Suna so su kawadda gurbacewar mahalli)
7. We want to get rid of sleeping late (Munaso mu daina yin bacci a makare)
8. The students have to get rid of exam malpractice (Daliban yakamata su kawadda satar jarrabawa)
Domin koyon turanci cikin sauki a hausance cikin tsarin mu na Online (WhatsApp) a duk inda kuke a duniya ku tuntube mu a +2348065586555
No comments:
Post a Comment