Anan zamuyi dubane ga yacce mutum zai yi amfani da gajeriyar jumla mai sigar tambaya ta “HOW OFTEN..” a cikin zance na turanci.
Akan yi amfani da ita don tambayar mutum akan adadin da yake aikata wani aiki da yake yi a yau da kullum.
Ga misalan ta a aikace
(A) In used (A aikace)
1. How often do you go to the market?
(kamar sau nawa ka/ki ke zuwa kasuwa?)
2. How often do you go to the school?
(kamar sau nawa ka/ki ke zuwa makaranta?)
3. How often do you go to the farm?
(kamar sau nawa ka/ki ke zuwa gona?)
4. How often do you visit him?
(kamar sau nawa ka/ki ke ziyartar sa?)
5. How often do you eat?
(kamar sau nawa ka/ki ke cin abinci?)
6. How often does he go for shopping?
(kamar sau nawa yake zuwa siyayya?)
7. How often does she cook?
(kamar sau nawa take girki?)
8. How often do they play football?
(kamar sau nawa su ke yin bal?)
9. How often does Ahmad wash his car?
(kamar sau nawa Ahmad yake wanke motar sa)
10. How often does Rahama do the dishes?
(kamar sau nawa Rahama take wanke wanke?)
(B) How to answer (Yacce mutum zai bada amsa)
1. I go to the market three times in a week
(ina zuwa kasuwa sau uku a sati)
2. I go to the school everyday
(ina zuwa makaranta a kullum)
3. I go to the farm on monthly basis
(ina zuwa gona wata wata)
4. I visit him on and off
(nakan ziyarce shi sama sama)
5. I eat three times daily
(nakan ci abinci sau uku a kullum)
6. He goes shopping on weekly basis
(yakan je siyayya duk sati)
7. She cooks twice daily
(takan yi girki sau biyu a rana)
8. They play football everyday
(sukan yi bal a kullum)
9. Ahmad washes his car daily
(Ahmad yana wanke motar sa kullum)
10. Rahama do the dishes daily
(Rahama takan yi wanke wanke kullum)
Domin koyon turanci cikin sauki a hausance cikin tsarin mu na Online (WhatsApp) a duk inda kuke a duniya ku tuntube mu a +2348065586555
No comments:
Post a Comment