Esay and Fastest Way to Learn

Esay and Fastest Way to Learn
Koyon turanci cikin sauki

Friday, 15 February 2019

“IT IS HIGH TIME” IN USED (‘IT IS HIGH TIME ' A AIKACE)

Anan zamuyi dubane ga yacce mutum zai yi amfani da gajeriyar jumla ta “IT IS HIGH TIME” a turance.
       Sau tari akan yi amfani da gajeriyar jumlar wajen nuni da cewa lokacin aikata wani aiki yayi, ma'ana lokaci yayi. Sannan akan takaita jumlar “It is high time” zuwa “It's high time” a baki da kuma a rubuce musamman ma idan mutum zai yi magana da 'yan uwansa, abokai ko kawaye da dangi.
           
          Ga misalan yacce ake amfani da ita a aikace:

1. It's high time to go home (Lokaci yayi na tafiya gida)

2. It's high time to get married (Lokaci yayi na yi aure)

3. It's high time to learn English (Lokaci yayi ki koyi turanci)

4. It's high time you start cooking (Lokaci yayi ka/ki fara girki)

5. It's high time to go work (Lokaci yayi na tafi aiki) 

6. It's high time you assist him (Lokaci yayi ka/ki taimake shi)

7. It's high time you get rid of smoking (Lokaci yayi ka/ki daina shaye shaye)

8. It's high time we sleep (Lokaci yayi muyi bacci)

9. It's high time they arrive here (Lokaci yayi su iso nan)

10. It's high time for Abdul to go to school (Lokacin Abdul yayi ya tafi makaranta)


Domin koyon turanci cikin sauki a hausance cikin tsarin mu na Online (WhatsApp) a duk inda kuke a duniya ku tuntube mu a +2348065586555

1 comment: