Esay and Fastest Way to Learn

Esay and Fastest Way to Learn
Koyon turanci cikin sauki

Saturday, 9 February 2019

HOW TO MAKE A COMPULSION TO YOUR SELF OR OTHERS IN ENGLISH (Yacce mutum zai tilastawa kansa ko ya tilastawa wasu a Turanci)

Sau tari mutum ya kan tilastawa kansa ko alkawartawa kansa ko wasu wani aiki ko wani abu da ya kamata yayi ko su yi.
Munada hanyoyi da dama da ake amfani dasu wajen tilastawa a kowanne yanayi da mutum zai iya tsintar kansa wajen magana a lokacin. wayan nan yanayi dai an kasasu kashi uku a takaice, sune yanayi na aikin da ake yanzu wanda muke kiransa da PRESENT TENSE sai kuma yanayi da yake nuni da aikin da wuce wato da ake kira PAST TENSE da kuma yanayin da yake nuni da aikin da za'a aikata nan gaba wato FUTURE TENSE
       Munada hanyoyi da ake amfani dasu a kowanne yanayi da muke dasu. Ga hanyoyin kamar haka:
📌PRESENT TENSE (YANAYI NA AIKIN YANZU): A wannan yanayi mukanyi amfani da HAVE TO wajen tilastawa kai ko wasu.
       Misali:


  • I have to go to school (Ya zama lallai naje makaranta)
  • You have to finish it (Ya zama lallai ka/ki kammala)
ABIN LURA:


  1. Akan yi amfani da kalmar MUST domin tilastawa kamar yacce ake amfani da kalmar HAVE TO. Misali: I must go to school (Dole naje makaranta) You must finish it (Dole ka/ki kammala)
  2. Akan yi amfani da HAS TO idan ana magana akan aikin da wani zai aikata alhalin baya wajen da ake magana a kansa.  Misali: She has to find it (Ya zama lallai ta nemo shi [abin] )

   📌PAST TENSE (YANAYIN  DA YAKE NUNI DA AIKIN DAYA GABATA): A wajen tilastawa kai ko wani akan aikin da aka riga aka kammala shi ko ya wuce misalin aikin da akayi dazu, jiya, makon daya wuce, watan daya wuce ko shekarar data wuce. A irin wannan yanayi mukanyi amfani da HAD TO
       Misali:


  • I had to go to school yesterday (Da lallai ya kamata naje makaranta jiya)
  • You had to finish it last week (Da lallai ya kamata ka/ki kammala a makon daya gabata)
    📌FUTURE TENSE (YANAYI NA AIKIN DA ZAI GUDANA): A wajen nuni ga aikin da lallai za'a aikata nan gaba kamar gobe, jibi, mako mai zuwa, shekara mai zuwa da sauransu mukanyi amfani da WILL HAVE TO.
          Misali:
  • I will have to go to school tomorrow (Lallai ya kamata naje makaranta gobe)
  • You will have to finish it tomorrow (Lallai yakamata ka/ki kammala gobe)
Ga sauran misalansu kamar haka:
(A) IN PRESENT TENSE (A yanayin da ake maganar sa a yanzu)
1. I have to wait for you (Ya zama lallai na jira ka/ki)
2. I have to cook the food (Ya zama lallai nayi girkin)
3. I have to read my book (Ya zama lallai na karanta littafi na)
4. I have to help them (Ya zama lallai na taimakesu)
5. I have to pay the money (Ya zama lallai na biya kudin)
6. You have to complete this work (Ya zama lallai ka/ki kammala aikin nan) 
7. You have know  his name (Ya zama lallai ka/ki san sunan shi)
8. They have wait for us (Ya zama lallai su jira mu) 
9. They have to clean the place (Ya zama lallai su goge wajen)
10. She has to follow us (Ya zama lallai ta biyo mu) 
11. She has to copy it (Ya zama lallai ta kwafe shi [abin] )
12. He has repair the car (Ya zama dole ya gyara motar)
13. He has to go him (Ya zama lallai  yabi shi)
14. We have to go to the market (Ya zama lallai mu tafi kasuwa)
15. We have to go now (Ya zama lallai mu tafi yanzu)
16. I must let them know (Dole na bari su sani)
17. You must sweep the room (Dole ka/ki share dakin)
18. He must go to travel to Dubai (Dole yayi tafiya zuwa Dubai)
19. They must beat him (Dole su zane shi)
20. We must help our selves (Dole mu taimaki kanmu)

(B) IN PAST TENSE (A yanayi na aikin da ya gudana a baya)
1. I had to go to the hospital (Da lallai ya kamata naje asibiti)
2. I had to let them know (Da lallai ya kamata na barsu su sani)
3. He had to call them yesterday (Da lallai yakamata ya kirasu jiya)
4. She had to finish last night (Da lallai ya kamata ta gama daren jiya)
5. We had to send him yesterday (Da lallai yakamata mu turashi jiya)

(C) IN FUTURE TENSE (A yanayi na aikin da zai wakana a gaba)
1. I will have to marry Amina (Lallai kamata na auri Amina)
2. I will have to comply with them (Lallai yakamata na yarda da yacce suke so)
3. She will have to cook for us (Lallai yakamata tayi mana girki)
4. We will have to find out (Lallai yakamata mu gano dalilin)
5. They will have to come with us (Lallai yakamata su taho tare damu)

Domin koyon turanci cikin sauki a hausance cikin tsari mai kyau a duk inda kuke a duniya  ku tuntube mu a +2348065586555

3 comments: