Anan zamuyi dubane ga yacce mutum zaiyi amfani da gajeriyar jumla ta “NEED NOT” a turance.
Mukanyi amfani da gajeriyar jumla ta need not wajen nuni ga abin da yake ba dole.Wato abin da bai zama tilas mutum ya aikatashi ba a yanayi na yanzu ko yanayin da zai zo nan gaba.
Ga misalan yacce ake amfani da ita:
1. You need not see him (Ba dole bane ka/ki ganshi)
2. You need not go to the hospital (Ba dole bane ka/ki je asibiti)
3. You need not write the note (Ba dole bane ka/ki rubuta)
4. You need not buy beat her (Ba sai ka/kin dake ta ba)
5. You need not cook (Ba sai kinyi girki ba)
6. You need not travel now (Ba sai ka/kin yi tafiya yanzu ba)
7. You need not call him (Ba sai ka/kin kirashi ba)
8. He need not wash the car (Ba sai ka/kin wanke motar ba)
9. She need not beat the boy (Ba sai ta daki yaron ba)
10. We need not complete the work Ba sai mun kammala aikin ba)
Domin register damu don koyon turanci cikin sauki ta hanyar waya (WhatsApp) a duk inda kuke a duniya ku nemi mu a +2348065586555. Sai mun jiku.