Esay and Fastest Way to Learn

Esay and Fastest Way to Learn
Koyon turanci cikin sauki

Thursday, 31 January 2019

MAKING FORMAL REQUEST AND PERMISSION (Use of Could/Amfani da Could don neman biyan bukata ko kuma izini)

  •  Could
Hanya ta Uku da ake amfani da ita wajen neman biyan bukata ko kuma izini ita ce hanyar
amfani da kalmar Could. Ana amfani da ita ne sosai a hukumance ko wajen magana da wanda ya girme ka/ki. Amfi so ayi amfani da ita don nuna cikakkiyar girmamawa ga wanda ake magana da shi.
  
        Ga misalan inda zakuyi amfani da ita kamar haka:
  1. Could I make a call? (shin wai zan iya yin kira?)
  2. Could you please open the door? (shin wai za ka/ki iya bude kofar?)
  3. Could you turn down the music? (shin wai za ka/ki iya rage sautin kidan?)
  4. Could you tell me what time it is? (shin wai za ka/ki iya gayamin lokaci?)
  5. Could I take one? (shin wai zan iya daukar guda/daya?)
  6. Could I ask a question? (shin wai zan iya tambaya?)
  7. Could we go home now? (shin wai zamu iya tafiya gida yanzu?)
  8. Could you take the message please? (shin wai za ka/ki iya karbar sakon?)
  9. Could you carry this for me? (shin wai za ka/ki iya daukar min wannan[abu]?)
  10. Could I pay the money for the goods? (shin wai zan iya biyan kudin kayan?)

Wednesday, 30 January 2019

MAKING A FORMAL REQUEST AND PERMISSIONS (Use of May/ Amfani da kalmar May)

  • May
 May Itama kalma ce da ake amfani da ita wajen neman izini kamar yadda ake amfani da Can har ma sau tari akan fi amfani da ita don neman izini wajen wanda ya girme ka/ki fiye da yar uwarta Can.

     Ga misalai da kalmar May kamar haka:

  1. May I see it? (shin zan iya ganin sa [abu]?)
  2. May I wait for you? (shin zan iya jiran ka/ki?)
  3. May I wait here? (shin zan iya jira anan?)
  4. May I sit with you? (shin zan iya zama tare da kai/ke?)
  5. May I invite him? (shin zan iya gayyatar sa?)
  6. May I bring it? (shin zan iya kawo shi [abu]?)
  7. May I take it? (shin zan iya daukar sa [abu]?)
  8. May I buy the food? (shin zan iya sayo abinci?)
  9. May I go to the bank? (shin zan iya zuwa banki)
  10. May I go to the hospital? (shin zan iya zuwa asibiti?)
  11. May I go to his house? (shin zan iya zuwa gidanshi?)
  12. May I go to the event? (shin zan iya zuwa taron?)
  13. May I come in? (shin zan iya shigowa ciki?)
  14. May I know your name? (shin zan iya sanin sunan ka/ki?)
  15. May I accompany you? (shin zan iya raka ka/ki)

Tuesday, 29 January 2019