Esay and Fastest Way to Learn

Esay and Fastest Way to Learn
Koyon turanci cikin sauki

Wednesday, 12 September 2018

MATAKAI / AZUZUWAN DA MUKA TANADA

 Muna sanarwa da masu sha'awar shiga tsarin namu da cewa mun tanadar muku matakan karatun ko muce aji guda uku, muna son mutum ya zabi daya daga cikin matakan/aji (wato mataki na farko ko na biyu ko kuma na Uku) dai dai da yanayin matakin sa na karatu kuma yake so a fara masa, dake kasa:-

1. Munada mataki koyarwa na farko da muke kira Pre-Basic (wannan mataki shine wanda zamu farawa mutum karatu tun daga ABCD).

2. Mataki na biyu shine mataki na tsakiya wanda muke Kira da Basic (wannan mataki shine na wa'yanda suka iya rubutu da karatu kuma sukanji wani abu a turanci amma basa iya mayarwa).

3. Sai mataki na karshe shine matakin masu neman kwarewa a fannin turanci shi muke kira da Post-Basic (wanna mataki shine na 'yan makarantar gaba da sakandire, wato masu neman horo wajen karin sani a fannin turanci da wajen magana a cikin jama'a. Samun Karin kalmomin turanci da salo na turanci don samun cikakkiyar kwarewa a harshen turanci).

2 comments:

  1. Wannan sune matakan da muke da su. Yanzu haka munada dalibai da muka fara kowanna mataki dasu suna daukar darussa a wajen mu. Kuma suna godiya domin suna ganewa sosai.

    ReplyDelete