Ga duk wanda Allah yasa yayi rigista damu zai sami dama kamar haka:-
- A tsarin da mukeso ya kasance wajen koyar daku shine mutum ya ware lokaci wato sa'a guda a ranakun LITININ zuwa JUMA'A don koyar daku har tsahon kwanaki sittin. To amma idan aka sami akasi baku hau Online ba a lokacin da kuka ware don yin darasi damu sakamakon rashin lafiya, rashin data ko kuma rashin chaji, ko kuma wani muhimmin uzuri yasha gabanku kamar biki, suna ko kuma rubuta jarabawa ga dalibanmu a makarantunsu. To a wannan hali zamu tsaida darasinku har sai komai ya daidaita atare daku don mu koyar daku cikin yanayi mai kyau.
- Zamu taimakawa dalibanmu musamman yan makaranta wajen koya musu Assignment din da yafi karfinsu. Kokuma muyi musu karin bayani a kowanna fanni da basu gane ba cikin al'amuran karatunsu. Hakan zai yiwu ne ta hanyar malamin da mutum ya zaba, dalibin kawai zai rubutowa malaminsa tambayoyin ko ya dau hoton tambaya ko kuma abin da yake neman karin bayani akai, shi kuma malamin zai yi kokari ya turo masa da amsa cikin kankanin lokaci.
- Ga iyaye mata munyi musu tanadi na cewa idan an bawa yaransu Assignment a makarantunsu kuma Su bazasu iya amsa musu ba. To suma sunada damar da zasu sanarwa da malami ko malamarsu don share musu hawaye take.
- Zamu taimakawa dalibanmu yan makarantar gaba da sakandire da shawarwarin akan rubutunsu na Project ko kuma masu Teaching Practice da sauran abubuwa na makaranta. Wannan taimako zasu samu ne ta hannun malamansu.
- Hakazakila idan mutum yanada tambaya akan darasin da mukayi masa ko kuma neman karin bayani akan wasu abubuwan, toh ko da yaushe ya nememu InshaAllah zamu bashi amsar abin da yake so.
- Akwai damar da koyaushe mutum yake neman shawarar mu cikin harkokinsa ga al'amuran da suka sha masa gaba, muyi kokari mu samarmasa da gamshashshiyar shawara da zata warware masa yanayin da yake ciki.
No comments:
Post a Comment