Esay and Fastest Way to Learn

Esay and Fastest Way to Learn
Koyon turanci cikin sauki

Wednesday, 12 September 2018

MATAKAI / AZUZUWAN DA MUKA TANADA

 Muna sanarwa da masu sha'awar shiga tsarin namu da cewa mun tanadar muku matakan karatun ko muce aji guda uku, muna son mutum ya zabi daya daga cikin matakan/aji (wato mataki na farko ko na biyu ko kuma na Uku) dai dai da yanayin matakin sa na karatu kuma yake so a fara masa, dake kasa:-

1. Munada mataki koyarwa na farko da muke kira Pre-Basic (wannan mataki shine wanda zamu farawa mutum karatu tun daga ABCD).

2. Mataki na biyu shine mataki na tsakiya wanda muke Kira da Basic (wannan mataki shine na wa'yanda suka iya rubutu da karatu kuma sukanji wani abu a turanci amma basa iya mayarwa).

3. Sai mataki na karshe shine matakin masu neman kwarewa a fannin turanci shi muke kira da Post-Basic (wanna mataki shine na 'yan makarantar gaba da sakandire, wato masu neman horo wajen karin sani a fannin turanci da wajen magana a cikin jama'a. Samun Karin kalmomin turanci da salo na turanci don samun cikakkiyar kwarewa a harshen turanci).

YACCE MUKE KOYARWA TA DANDALIN SADA ZUMUNTA NA WhatsApp


    1. Da farko mukan turo muku da darasinku a rubuce.
     2. Sai mu umarceku da ku rubuta darasin a littafin rubutunku.
     3. Daganan sai mu yi muku bayani ta hanyar turo muku sako ta voice note
     4. Daga bisani sai mu tambayeku akan fahimtarku gameda darasin da muka gabatar.
     5. Bacin kun amsa, wato mun tabbata kun  fahimci darasin da muka gabatar sai mu turo muku AUDIO lesson, wato idan ya kasance darasin mai audio ne. 
     6. Daga nan sai muyi muku tambayoyi game da darasin don mu sami tabbacin fahimtar ku ga darasin.
     7. Daga karshe mukan bukaci da ku karanto mana darasin don mu tabbata lallai kun iya darasin daya gabata.  

Tuesday, 11 September 2018

SUWAYE DALIBANMU?

Dalibanmu sun kasance maza da mata daga kowanna fadi da sassan duniya matukar mutum yana jin yaren HAUSA.

DAMAR DA ZAKU SAMU

Ga duk wanda Allah yasa yayi rigista damu zai sami dama kamar haka:-
  • A tsarin da mukeso ya kasance wajen koyar daku shine mutum ya ware lokaci wato sa'a guda a ranakun LITININ zuwa JUMA'A don koyar daku har tsahon kwanaki sittin. To amma idan aka sami akasi baku hau Online ba a lokacin da kuka ware don yin darasi damu sakamakon rashin lafiya, rashin data ko kuma rashin chaji, ko kuma wani muhimmin uzuri yasha gabanku kamar biki, suna ko kuma rubuta jarabawa ga dalibanmu a makarantunsu. To a wannan hali zamu tsaida darasinku har sai komai ya daidaita atare daku don mu koyar daku cikin yanayi mai kyau.
  • Zamu taimakawa dalibanmu musamman yan makaranta wajen koya musu Assignment din da yafi karfinsu. Kokuma muyi musu karin bayani a kowanna fanni da basu gane ba cikin al'amuran karatunsu. Hakan zai yiwu ne ta hanyar malamin da mutum ya zaba, dalibin kawai zai rubutowa malaminsa tambayoyin ko ya dau hoton tambaya ko kuma abin da yake neman karin bayani akai, shi kuma malamin zai yi kokari ya turo masa da amsa cikin kankanin lokaci.
  • Ga iyaye mata munyi musu tanadi na cewa idan an bawa yaransu Assignment a makarantunsu kuma Su bazasu iya amsa musu ba. To suma sunada damar da zasu sanarwa da malami ko malamarsu don share musu hawaye take.
  • Zamu taimakawa dalibanmu yan makarantar gaba da sakandire da shawarwarin akan rubutunsu na Project ko kuma masu Teaching Practice da sauran abubuwa na makaranta. Wannan taimako zasu samu ne ta hannun malamansu.
  • Hakazakila idan mutum yanada tambaya akan darasin da mukayi masa ko kuma neman karin bayani akan wasu abubuwan, toh ko da yaushe ya nememu InshaAllah zamu bashi amsar abin da yake so. 
  • Akwai damar da koyaushe mutum yake neman shawarar mu cikin harkokinsa ga al'amuran da suka sha masa gaba, muyi kokari mu samarmasa da gamshashshiyar shawara da zata warware masa yanayin da yake ciki.

JADAWALIN KOYARWA

1. RANAKUN LITININ;- Ranaku ne da mukan gudanar da darussa na tsahon sa'a guda. Bacin kun zabi lokacin da kukeso na darasin.
2. RANAKUN TALATA;- Ranaku ne da mukan gudanar da darussa kamar ranar data gabata.
3. RANAKUN LARABA;- Ranaku ne da mukan bada darussa kamar yadda aka saba. Amma mukan bada fifiko wajen koyar daku furucin kalmomi cikin harshen Turanci.
4. RANAKUN ALHAMIS;- Rana kune da mukan gudanar da darussa kamar yau da kullum.
5. RANAKUN JUMA'A;- Rana kune da mukan gudanar da darussa kamar yacce muka saba.
6. RANAKUN ASABAR;- Wannan rana bama gudanar da darussa, ma'ana ranace ta hutu. Sai dai mukan baku dama da ku shigo dandalinmu kuna tattaunawa ta hanyar murya (wato, Voice note) domin ku goge wajen iya furta kalmomi.
7. RANAKUN LAHADI;- Wannan rana ranar hutu ce da muka tanadar muku don kuyi bitar darussan da sauka gabata cikin satin da ya shude.

TSARIN KOYARWAR MU

Ga duk wanda ya sami damar yin register damu to zamu bashi zabin malami ko malama da zasu dunga yin darasi. Sannan kuma mutum zai zabi lokacin da yayi masa (Safe, Rana ko Dare) a ranakun LITININ zuwa JUMA'A wanda za'ayi masa darasinsa, wato awa guda da zai zaba yacce za ake masa karatu tare da daya daga cikin malaman mu da muka tanadar muku da zakuyi darasin tare.

Sunday, 9 September 2018

TSARIN RIGISTA DAMU

Ga maison yin register damu don a fara masa darasi ko kuma Neman Karin bayani zai iya tuntubarmu ta lambar waya kamar haka:  +2348065586555 +2348155337326. Ta hanyar Kira kai tsaye ko ta hanyar magana ta WhatsApp. Ko kuma ta e-mail wato; talamiz2015@gmail.com Mungode saimun jiku.

HANYAR KOYARWAR MU

Munyi duba ga hanyar da akafi amfani da ita a halin yanzu domin sadarwa. Wato ta dandalin sada zumunta na WhatsApp. Ta hanyar WhatsApp zamu koyar da ku kuma ku fahimta kamar kuna gabammu. Domin tsare tsare sunyi nisa don yanzu haka mun fara gudanar da tsarin koyarwar ga mutane da dama na sassan Nigeria da kuma wasu daga kasashen ketare kamar su Niger, Chadi, Kamaru da sauransu.

TANADIN DA MUKAYI MUKU

A tsarin na koyar da harshen turanci mun tanadar muku kwararrun malamai da suka goge ta fannin koyar da harshen turanci shekara da shekaru. Muna farincikin sanar muku da cewa cikin kwanaki sittin da muka tsara zaku iya harshen turanci ga masu koyo daga tushe ko kuma ku kware sosai wato ga masu Neman kwarewa a fannin harshen turanci sosai cikin wata biyu kachal.

SABON ALBISHIR


Muna muku albishir da cewa mun shigo da sabon tsarin koyar da harshen turanci ta online. wannan tsari sabo ne a Nigeria amma wasu kasashen da suka cigaba sun dade suna gudanar dashi kamar kasar Indiya, China, Brazil, South Africa, Uganda, Kenya da sauransu kasashe da dama a fadin duniya. Tsarine da kana gida ko kina gida a zaune ko ma a kwance kana daukar darasi cikin hanyoyi masu sauki.