Esay and Fastest Way to Learn

Esay and Fastest Way to Learn
Koyon turanci cikin sauki

Thursday, 1 September 2022

PHRASAL VERBS

 🛑 ''PHRASAL VERBS''


Gabatarwa (Introduction)

''Phrasal Verbs'' wani jigo ne a harshen Turanci domin suna ɗaya daga cikin abubuwan da dole mutum ya sansu domin iyawa da kwarewa a cikin harshen Turanci. Domin ina muka dauki harshen Turanci gaba ɗaya, muna iya rabashi kaso kamar;


❇️ GRAMMAR - Sannin dokiki da ƙa'idodin harshen Turanci.

❇️VOCABULARY - Sanin kalmomin Turanci.

❇️ IDIOMS - Sanin salon magana na harshen Turanci

❇️ PHRASAL VERBS - Sanin tasarrafin harshen Turanci.

❇️ LITERATURE - Sanin adabi na Turanci.

  

 Idan mukayi duba zamuga mun kasa manyan ɓangarori na gaba ɗaya harshen Turanci guda biyar (5) wanda ɗaya daga cikinsu shine ''Phrasal Verbs'' wato ilimi akan sani na tasarrafin harshen Turanci, kuma ya kasance jigone babba da idan har kana buƙatar ka iya kuma ka kware a harshen Turanci dole ne kasan da yawa daga ''Phrasal Verbs''.

         Misali; mu ɗauki wannan ƙunshin kalmomi ''abide by'' wanda ɗaya ne daga cikin phrasl verbs da muke dasu zamuga kalmomi biyune suka taru suka haɗa su, wato kalmar (abide) da kuma kalmar (by) wanda ita kalmar ''abide'' ta kasance ɗaya daga cikin jinsi ne na aikatau wato (verb) wato wannan ya shafi ɓangaren grammar a Turanci, sai kuma ɗaya kalmar ta ''by'' wadda ta kasance ɗaya daga cikin wasu jinsi a fannin ilimin grammar da ake kira da (preposition) to anan zamuga cewa ginshiƙin PHRASAL VERBS ansamo sune daga cikin GRAMMAR sai dai suma suna cin gashin kansu kamar sauran ginshiƙai na Turanci. Sannan kuma zamuga cewa abu biyu ne yawanci suke haɗuwa waje guda su haɗa ''PHRASAL VERBS'' wannan ba komai bane face (Preposition + Verb)  shi yasa ma akayi la'akari da furucin su aka kirasu da ''PHRASAL VERBS''.

            ''Phrasal Verb'' guntuwar jumla ce Mara cikakkiyar ma'ana da ake dunkule su a kirasu da ''phrase'' don haka gaba ɗaya PHRASAL VERBS da ake dasu basa bada cikakkiyar ma'ana su kaɗai dole sai an haɗasu da wasu kalmomin sun bada doguwar jumla mai ma'ana. Misali, wannan phrasal verb na ''abide by'' baya bada cikakkiyar ma'ana dole sai anyi amfani dasu a cikin jumla (sentence) wanda zamu dubasu a darasin mu na gaba.

      PHRASAL VERBS na da matuƙar yawa da gaske amma inshaAllah zamuyi duba akan mafi yawa daga cikinsu, duba na tsakanaki domin a sansu kuma a iya amfani dasu a Turanci saboda muhimmacin da suke a Turanci wanda zan ƙara jaddadawa cewa idan har baka sansu ba to fa sai nayi maka rantsuwa wallahi baka iya Turanci ba. Ku biyo mu domin muyi karatu akansu na tsakanaki.


🔰Muna so Don Allah idan har kazo karshe a karatun nan kuyi:

📌 Share

📌 Like 

     Sannan idan kunada da tambaya ko  ƙarin bayani, mu haɗu a comment section.


Director (TALAMIZ ENGLISH)✍️




Monday, 29 November 2021

PRONUNCIATION OF THE WORD ''ISLAND'' - FURUCIN KALMAR ''ISLAND''

 


👨🏻‍🏫PRONUNCIATION - FURUCI


⚜️ISLAND - Tsibiri

👄(I-land)


⚠️ Note: S is silent (Tunatarwa: S ba'a furta ta)


✍️Examples - Misali


(1) Japan is an island country.

 -Japan kasace a tsibiri.


(2) Umar walked around the island.

 -Umar yayi tattaki a tsibirin.


(3) You can't live on that island.

 -Ba za ka/ki iya rayuwa a wannan tsibirin ba.


(4) I think we're the only people on this island.

 -Ina tunani fa mune kadai mutane a wannan tsibirin.


(5) Greece has many islands.

 -Kasar Greece tana da tsibirai da yawa.


(6) Who discovered the island?

 -Waye ya gano tsibirin?


(7) There is only one road on the island.

 -Hanya daya ce kawai a tsibirin.


📍📍📍📍📍📍📍📍📍📍📍📍📍


🔠Words & Phares Used:

(Kalmomi da Karamar jimla da akayi amfani dashi)


- I (Ni)


- You (Kai/ke)


- Island (Tsibiri)


- Country (Kasa)


- Walk (Tafiya, idan lokacin da akayi tafiyar ya wauce ''ma'ana Past tense'' zai koma ''Walked'')


- Around (Kewaye, Gurbi)


- Can't (Takaitawa ne, ma'ana short form na ''Can not'' ) Yana nuni da rashin yin abu.


- Live (Rayuwa)


- Only (Kadai, tal, jal)


- People (Mutane)


- Many (Dayawa)


- Who (Ways/wanene)


- Discover (Ganowa/bincikowa, idan lokacin share a gano abin ya wauce ''ma'ana Past tense'' zai koma ''Discovered'')


- One (Daya)


🔰 If you find it useful, please like👍, comment📝 and share ➡️


🔰Idan ka amfana da wannan, ku danna like👍 kuyi comment📝 sannan kuyi share ➡️


©️TALAMIZ ENGLISH 2021


Thursday, 25 November 2021

PRONUNCIATION OF THE WORD ''WEDNESDAY'' - FURUCIN KALMAR ''WEDNESDAY''

 



👨🏻‍🏫PRONUNCIATION - FURUCI


⚜️WEDNESDAY - Ranar Laraba

👄(Wenz-day/Wenz-de)


⚠️ Note: The letter ''W'' in Wednesday is always written in Capital letter (Tunatarwa: Harafin ''W'' na cikin kalmar Wednesday ana rubuta shi a ko yaushe da babban baki)


✍️Examples - Misali


(1) It's Wednesday.

 -Ranar Laraba ce.


(2) Today is Wednesday.

 -Yau ranar Laraba ce.


(3) I have work on Wednesday.

 -Ina da aiki ranar Laraba.


(4) I will see you on Wednesday.

 -Zan hadu da kai/ke ranar Laraba.


(5) Are you free on Wednesday?

 -Shin ka/ki na da lokaci ranar Laraba?


(6) Will you come on Wednesday?

 -Shin za ka/ki zo ranar Laraba.


(7) Wednesday is my day off

 -Ranar Laraba itace ranar hutu na.


(8) She has been absent since last Wednesday.

 -Ta kasance bata nan tun Larabar data gabata.


(9) She has been sick since last Wednesday.

 -Ta kasance tana cikin rashin lafiya run Larabar data gabata.


(10) We have to submit our books on Wednesday.

 -Yakamata mu kai littattafan mu ranar Laraba.


📍📍📍📍📍📍📍📍📍📍📍📍📍📍📍


🔠Words & Phares Used:

(Kalmomi da Karamar jimla da akayi amfani dashi)


- I (Ni)


- You (Kai/ke)


- Your (Naka /naki)


- Wednesday (Ranar Laraba)


- Today (Yau)


- I have (Ina da)


- Work (Aiki)


- I will (Zan)


- See (Gani/haduwa)


- Are you... (Shin ka/ki na...)


- Free (Yanayi na rashin aiki ko hutu)


- Will you (Shin za ka/ki)


- Come (Zo)


- Day off (Ranar hutu)


- She has been (Ta kasance)


- Absent (Fashi)


- Since (Tun)


- Last (Na karshe/karshe)


- Sick (Rashin lafiya)


- We have to.. (Ya kamata mu..)


- Submit (Kai sako/kaiwa)


- Our (Namu)


- Books (Litattattafai)


🔰 If you find it useful, please like👍, comment📝 and share↪️


🔰Idan ka amfana da wannan, ku danna like👍 kuyi comment📝 sannan kuyi share↪️

Monday, 22 November 2021

PRONUNCIATION OF THE WORD ''RECEIPT'' - FURUCIN KALMAR ''RECEIPT''

 



👨🏻‍🏫PRONUNCIATION - FURUCI


⚜️RECEIPT - Rasit/Rasiti

👄(Ree-seet/Rii-siit)


⚠️ Note: P is silent (Tunatarwa: P ba'a furta ta)


✍️Examples - Misali

(1) I asked for a receipt.

 -Na tambayi rasitin.

(2) Do you have a receipt?

 -Ka/ki na da rasiti?

(3) The receipt is your proof of purchase.

 -Rasitin shine shaidar ka/ki na sayayyar { da ka/kika yi}

(4) The receipt shows details of the item purchased.

 -Rasitin ya nuna bayanan kayan da aka siya.

(5) Keep the receipt as a proof of purchase.

 -Ajiye rasitin a matsayin shaidar siyayyar.

(6) Can I have a receipt, please?

 -Shin zan iya samun rasiti?

📍📍📍📍📍📍📍📍📍📍📍📍📍


🔠Words & Phares Used:

(Kalmomi da Karamar jimla da akayi amfani dashi)


- I (Ni)


- You (Kai/ke)


- Your (Naka /naki)


- Receipt (Rasiti)


- Ask (Tambaya, idan lokacin ya wauce ''ma'ana Past tense'' zai koma Asked)


- Proof (Shaida/hujja)


- Show (Nunawa)


- Details (Bayanai)


- Items (Abubuwan da aka siya)


- Purchase (Siya, idan lokacin ya wuce ''ma'ana past tense'' zai koma purchased)


- Please (Kalmar roko ''muna iya fasaarata da kamar ace Don Allah'')


- Keep (Ajiyewa)


- Do you have...(Ka/ki na da...

- Can I have...(Zan iya samun...


🔰 If you find it useful, please like👍, comment📝 and share↪️


🔰Idan ka amfana da wannan, ku danna like👍 kuyi comment📝 sannan kuyi share↪️


©️ TALAMIZ CENTER 2021  📲+2348065586555

Monday, 1 April 2019

ASKING ABOUT CERTAINTY (Tamabaya akan tabbaci)

Anan zamuyi dubane ga yacce mutum zai yi tambaya akan tabbacin abu kamar faduwar sa, samuwar sa ko wanzuwar sa.
      Akwai hanyoyi da dama da ake amfani dasu wajen yin tambaya akan tabbacin abu.
      Ga kadan daga cikin hanyoyin:
(a) Do you think...(Shin ka/ki na da yakinin...)
(b) Do you believe...(Shin ka/kin yarda...)
(c) Are you sure...(Ka/Ki nada tabbaci...)
(d) Can you show me...(Za ka/ki iya nuna min/ shaida min)

Note/Tunatarwa:
A sama, Do you think ba yana nufin "Shin kayi tunani ba"

     Ga wasu misalan yacce ake amfani dasu a jumlace:
(1) Do you think he will come? (Shin ka/ki na da yakinin zai zo)
(2) Do you think she will help us? (Shin ka/ki na da yakinin zata taimakemu?)
(3) Do you think I will pass the exam? (Shin ka/ki na da yakinin zan ci jarabawa)
(4) Do you think the doctor will come by 9 O'clock (Shin ka/ki na da yakinin likitan zai zo da karfe tara)
(5) Do you think we can do it? (Shin kana tunanin zamu iya yin abin)
(6) Do you believe we can achieve it? (Shin ka/kin yarda cewa zamu iya kammala abin)
(7) Do you believe on this story? (Shin ka/kin yarda da labarin nan)
(8)Are you sure? (ka/kin tabbata)
(9) Are you sure he did the work? (Ka/ki nada tabbaci yayi aikin)
(10) Can you show me some more details (Za ka/ki iya nunamin wasu bayanan)


Domin yin register don koyon harshen turanci a saukake ku tuntube mu a +2348065586555

Wednesday, 27 February 2019

“NEED NOT” IN USED (Amfani da kalmar “Need not” a turanci)


Anan zamuyi dubane ga yacce mutum zaiyi amfani da gajeriyar jumla ta “NEED NOT” a turance.
     Mukanyi amfani da gajeriyar jumla ta need not wajen nuni ga abin da yake ba dole.Wato abin da bai zama tilas mutum ya aikatashi ba a yanayi na yanzu ko yanayin da zai zo nan gaba.
       
       Ga misalan yacce ake amfani da ita:
1. You need not see him (Ba dole bane ka/ki ganshi)
2. You need not go to the hospital (Ba dole bane ka/ki je asibiti)
3. You need not write the note (Ba dole bane ka/ki rubuta)
4. You need not buy beat her (Ba sai ka/kin dake ta ba)
5. You need not cook (Ba sai kinyi girki ba)
6. You need not travel now (Ba sai ka/kin yi tafiya yanzu ba)
7. You need not call him (Ba sai ka/kin kirashi ba)
8. He need not wash the car (Ba sai ka/kin wanke motar ba)
9. She need not beat the boy (Ba sai ta daki yaron ba)
10. We need not complete the work Ba sai mun kammala aikin ba)


Domin register damu don koyon turanci cikin sauki ta hanyar waya (WhatsApp) a duk inda kuke a duniya ku nemi mu a +2348065586555. Sai mun jiku.


Tuesday, 26 February 2019

“HOW DARE YOU” IN USED (Amfani da gajeriyar jumla ta “how dare you”)

Anan zamuyi dubane ga gajeriyar jumla ta “HOW DARE YOU” a cikin zance na yau da kullum.
     A kan fadi gajeriyar jumlar ne a lokacin da mutum yake cikin fushi a sakamakon abin da wani ya aikata wanda bai dace ba, ko shi bai isa ya aikata hakan ba. 
         Mukan fassara gajeriyar jumla ta “how dare you” da kai ka isa, kai waye, har ka kai, kai a su wa, da dai sauran su.
         Ga misalan yacce ake amfani da ita:
1. How dare you you abuse me (Kai ka isa ka zage ni)
2. How dare you come here (Har ka kai ka zo nan)
3. How dare you shout at me (Har ka isa ka yi min tsawa)
4. How dare you slap him (kai a su wa ka mare shi)
5. How dare beat me (kai a su wa ka dake ni)

Domin koyon turanci cikin sauki a hausance cikin tsari mai kyau a duk inda kuke a duniya  ku tuntube mu a +2348065586555


Sunday, 24 February 2019

“GET RID OF” IN USED (Yadda zamuyi amfani da gajeriyar jumla ta “get rid of”)

Anan zamuyi dubane ga yacce mutum zai yi amfani da gajeriyar jumla ta “GET RID OF” a Turance.
     Ana amfani da “get rid of” (wato: kawar da, gusar da, rabu da, ko tsai da) wajen nuni ga abin da mutum ya ga ya dace ya rabu dashi ko sun dace su rabu dashi ko ya daina ko su daina ko ya daina yin sa. Akan yi amfani da ita wajen kore abin da bashi da amfani don a daina aikatashi.
      
      Ga misalan yacce zamuyi amfani da ita:
1. You must get rid of him (Dole ka/ki rabu dashi)
2. You have to get rid of this stuff (Ya kamata ka/ki kawarda abubuwan nan)
3. You have to get rid of smoking (Ya kamata ka/ki rabu da shaye shaye)
4. I have to get rid of the waste (Ya kamata ta kawadda sharar)
5. I want to get rid of my sofa (Ina so na kawadda doguwar kujera ta)
6. They want to get rid of pollution (Suna so su kawadda gurbacewar mahalli)
7. We want to get rid of sleeping late (Munaso mu daina yin bacci a makare)
8. The students have to get rid of exam malpractice (Daliban yakamata su kawadda satar jarrabawa)


Domin koyon turanci cikin sauki a hausance cikin tsarin mu na Online (WhatsApp) a duk inda kuke a duniya ku tuntube mu a +2348065586555

Saturday, 23 February 2019

TELLING YOUR DISLIKES (Fadar abin da baka so)

Anan zamuyi dubane ga yacce mutum zai yi magana akan abin da baya so ko baya sha'awar amfani da shi ko aikatashi.
     Mukanyi amfani da gajeriyar jumla ta I DISLIKE  ko I HATE wajen nuni ga abin da mutum baya so ko baya burgeshi, baya sha'awar yi, amfani dashi ko aikatashi. Amma amfani da “I hate” na nuni ga cikakken rashin so na abu, ma'ana abin da mutum ya tsana sosai.
      Ga misalan yacce ake amfani dasu:
1. I dislike eating alone (banason cin abinci ni kadai)
2. I dislike his behavior (bana sha'awar halayyar sa)
3. I dislike her lateness (bana son lattin ta)
4. I dislike fish (bana son kifi)
5. I dislike him (bana son shi)
6. I hate him (na tsane shi)
7. I hate to see him (na tsani ganin shi)
8. I hate their policies (na tsani dokokin su)
9. I hate dirty things (na tsani abubuwa masu datti)
10. I hate to that woman (na tsani ganin waccen matar)

         San nan a takaice akanyi amfani da “I doesn't like” maimakon “I dislike” wajen nuni ga abin da mutum baya so ko baya sha'awa.

Domin koyon turanci cikin sauki a hausance cikin tsarin mu na Online (WhatsApp) a duk inda kuke a duniya ku tuntube mu a +2348065586555