Esay and Fastest Way to Learn

Esay and Fastest Way to Learn
Koyon turanci cikin sauki

Thursday, 14 February 2019

USE OF "HOW LONG..." IN A SENTENCE (Amfani da "how long.. " a cikin jumla)

Anan zamuyi dubane ga yacce mutum zai yi amfani da "HOW LONG...(Tsahon yaushe...)" a jumlace, saboda muhimmancin ta a yanayin zamantakewa na yau da kullum.
        Mukanyi amfani da "HOW LONG..." a kowanne yanayi da muke dasu wato yanayi da muke a yanzu (Present) ,  yanayin da ya wuce (Past) da kuma yanayin da zai zo (Future). Sai dai a kowanne yanayi a gaban How long dole mu saka TAKE TO

A yanayin da yake gudana a yanzu (Present)

      A nan mukan kara kalmar "Do" ko "Does" ko kuma "Can" a inda ya dace ayi amfani dasu tare da How long don tambaya ga abin da yake gudana a yanzu.
          
         Ga misalai kamar haka:
1. How long do you take to finish the work?
   (Tsahon wanna lokaci zai yi ka gama aikin nan?)

2. How long does he take to reach Lagos?

   (Tsahon wanna lokaci zai dauka ya isa Lagos?)

3. How long does she take to cook the food?

   (Tsahon wanna lokaci zata dauka tayi girkin?)

4. How long can we take to stay here? 

   (Tsahon wanna lokaci zamu dauka anan?)

5. How long can they take to finish the exam?

    (Tsahon wanna lokaci zasu dauka su yi jarrabawar?)


A yanayi na abin da ya wuce (Past)

      Ana mukanyi amfani da kalmar "DID" a gaban "HOW LONG" domin tambaya ga abin da ya gudana a baya.
         
         Ga misalai kamar haka:
1. How long did you take to finish the work?
   (Tsahon wanna lokaci ka dauka wajen kammala aikin?)

2. How long did he take to wash the clothes?

    (Tsahon wanna lokaci ya dauka wajen wanke kayan)

3. How long did she take to cook the food?

   (Tsahon wanna lokaci ta dauka wajen girkin)

4. How long did we take to complete the task?

   (Tsahon wanna lokaci muka dauka wajen kammala aikin)

5. How long did they take to finish the exam?

   (Tsahon wanna lokaci suka dauka wajen zana jarrabawar?)

A yanayi na aikin da za'a aikata nan gaba

        A wannan bangaren mukanyi amfani da kalmar WILL a gaban How long don tambaya akan tsahon lokacin da za'a dauka don aikata wani abin. 

       Ga misalai kamar haka:

1. How long will you take write the exam? 
    (Tsahon wanna lokaci zaka dauka kayi jarrabawar?)

2. How long will he take to repair the car?

    (Tsahon wanna lokaci zai dauka ya gyara motar?)

3. How long will she take to cook the food?

    (Tsahon wanna lokaci zata dauka tayi girkin)

4. How long will we take to finish the work?

    (Tsahon wanna lokaci zamu dauka mu kammala aikin?)

5. How long will they take to make the dress?

    (Tsahon wanna lokaci zasu dauka su dinka kayan)

DOMIN YIN REGISTER DAMU DON SHIGA TSARIN MU NA KOYAR DAKU HARSHEN TURANCI A HAUSANCE A TSARIN MU NA ONLINE A DUK INDA KUKE, KU NEME MU A +2348065586555

Wednesday, 13 February 2019

HOW TO TELL ABOUT REPEATED ACTIONS IN THE PAST (Yacce mutum zai yi magana akan abin da aka sha yinsa baya)

Anan zamuyi duba ne ga maganar da mutum zai yi akan abin da yake yawan yinsa a da ko wasu suke yawan aikatasu a baya amma a halin yanzu basa aikatashi.
        Mukanyi amfani da USED TO bayan mun fadi shi mai yin abin a baya kamar I, You, We, They ko kuma mu fadi sunan shi mai yin abin a fili.
     
               Ga misalai kamar haka:

1. I used to play football when I was young
    (ina yawan doka kwallo a lokacin da nake karami)

2. I used to study hard when I was at school
    (ina yawan karatu sosai a lokacin da nake makaranta)

3. He used to beat me when we are at school 
    (Yana yawan duka na a lokacin da muke makaranta)

4. She used to cook for us when we are young 
   (tana yawan yi mana girki a lokacin da muke yara)

5. We used to pay attention when we are students
    (mukan maida hankali a lokacin da muke dalibai)

6. They used to work with my father when he is at Kano
    (suna yawaita aiki da mahaifina a lokacin da yake a Kano)

7. Ahmad used to help his mother when he is just seven 
    (Ahmad yana yawan taimakawa mahaifiyar sa a lokacin da yake shekara bakwai)

8. Amina used to make the bed when she was young
   (Amina tana yawan gyara gado a lokacin da take karama)

9. Zainab used to make noise when we are students 
    (Zainab tana yawaita surutu a lokacin muna dalibai)

10. Musa used to buy rice before he get married 
     (Musa yana yawan siyan shinkafa kafin yayi aure)


Domin koyon turanci cikin sauki a hausance cikin tsari mai kyau a duk inda kuke a duniya  ku tuntube mu a +2348065586555

Tuesday, 12 February 2019

ASKING AND ANSWERING OF POSSESSION (Tambaya da amsa akan mallaka)

Anan zamuyi duba ne ga maganar da mutum zai yi akan abin da yake yawan yinsa a da ko wasu suke yawan aikatasu a baya amma a halin yanzu basa aikatashi.
        Mukanyi amfani da USED TO bayan mun fadi shi mai yin abin a baya kamar I, You, We, They ko kuma mu fadi sunan shi mai yin abin a fili.
     
               Ga misalai kamar haka:

1. I used to play football when I was young
    (ina yawan doka kwallo a lokacin da nake karami)

2. I used to study hard when I was at school
    (ina yawan karatu sosai a lokacin da nake makaranta)

3. He used to beat me when we are at school 
    (Yana yawan duka na a lokacin da muke makaranta)

4. She used to cook for us when we are young 
   (tana yawan yi mana girki a lokacin da muke yara)

5. We used to pay attention when we are students
    (mukan maida hankali a lokacin da muke dalibai)

6. They used to work with my father when he is at Kano
    (suna yawaita aiki da mahaifina a lokacin da yake a Kano)

7. Ahmad used to help his mother when he is just seven 
    (Ahmad yana yawan taimakawa mahaifiyar sa a lokacin da yake shekara bakwai)

8. Amina used to make the bed when she was young
   (Amina tana yawan gyara gado a lokacin da take karama)

9. Zainab used to make noise when we are students 
    (Zainab tana yawaita surutu a lokacin muna dalibai)

10. Musa used to buy rice before he get married 
     (Musa yana yawan siyan shinkafa kafin yayi aure)


Domin koyon turanci cikin sauki a hausance cikin tsari mai kyau a duk inda kuke a duniya  ku tuntube mu a +2348065586555

Monday, 11 February 2019

ASKING AND ANSWERING FOR WISHES (Tambaya da amsa bukata)

Anan zamuyi dubane ga yacce mutum zai tambayi wani nasa kamar mutanen gida, 'yan uwa, abokai ko baki wani lokacin ma harda abokan aiki ko abokan kasuwanci akan abin da suke bukata. Sannan zamuyi duba ga yacce mutum zai amsa idan an fada masa.
       A turance mukanyi amfani da WOULD YOU LIKE  don nuni ga abin da mutum yake bukata, sha'awa ko yake so. 
       
     Ga misalai kamar haka:
1. Would you like to go home? 
    (Shin ka/ki na bukatar zuwa gida?) 

2. Would you like to have some food?

    (Shin ka/ki na bukatar abinci?)

3. Would you like to visit him?

    (Shin ka/ki na bukatar ziyarsa?)

4. Would you like to have some water?

     (Shin ka/ki na bukatar shan ruwa?)

5. Would you like to travel by car?

     (Shin ka/ki na bukatar yin tafiya?)

6. Would you like to buy the rice?

     (Shin ka/ki na bukatar shinkafa?)

7. What would you like to eat?

     (Me ka/ki ke bukatar ci?)

8. What would you like do? 

     (Me ka/ki ke bukatar yi?)

9. What would you like to buy?

     (Me ka/ki ke bukatar siya?)

10. Where would you like to go?

      (Ina ka/ki ke bukatar zuwa?)

11. Where would you like to meet him?

      (Ina ka/ki ke bukatar haduwa da shi?)

12. When would you to travel?

      (Yaushe ka/ki ke bukatar yin tafiya?)

13. When would you like to marry her?

      (Yaushe ka/ki ke bukatar auren ta?)

14. Which would you like to take?

      (Wanne ka/ki ke bukatar dauka?)

15. Which would you like to buy?

      (Wanne ka/ki ke bukatar siya?)

            

              How to answer for wishes 
         (Yacce mutum zai amsa bukata)

1.Yes, I would like to go home 

   (Eh, ina bukatar zuwa gida)

2. Yes, I would like to have rice

    (Eh, ina bukatar cin shinkafa)

3. Yes, I would like to visit him 

    (Eh, ina bukatar na kai masa ziyara)

4. No, I wouldn't like some water

    (A,a bana bukatar ruwa)

5. No, I wouldn't like to travel by car 

    (A,a bana bukatar tafiya a mota)

6. No, I  wouldn't like to buy the rice?

    (A,a bana bukatar siyan shinkafa)

7. I would like to eat meet

    (Ina bukatar na ci nama)

8. I would like to sleep

   (Ina bukatar yin bacci)

9. I would like to buy an orange

   (Ina bukatar siyan lemo)

10. I would like to go to the market

     (Ina bukatar zuwa kasuwa)

11. I would like to meet him at home 

     (Ina bukatar haduwa da shi a gida)

12. I would like to travel tomorrow

      (Ina bukatar yin tafiya gobe)

13. I would like to marry her next year

  (Ina bukatar auren ta a shekara mai zuwa)

14. I would like to take the red one

     (Ina bukatar daukar jan[abin])

15. I would like to buy the bigger one

     (Ina bukatar siyan babban[abin])


Domin koyon turanci cikin sauki a hausance cikin tsari mai kyau a duk inda kuke a duniya  ku tuntube mu a +2348065586555

Sunday, 10 February 2019

TELLING ABOUT POSSIBILlTY (magana akan abin da zai iya faruwa)

A wani lokaci mukan bayyana abin da zai iya faruwa garemu ko ga wanda muke tare dasu a yanayi na zamantakewa.
Mukanyi amfani da kalmomin CAN, MAY da MIGHT wajen nuni ga abin da zai iya wakana.

  • CAN da MAY sukan fayyace abin da tabbas zai iya wakana, ma'ana abin da munada tabbacin faruwarsa.
  • MIGHT a daya hannun akanyi amfani da ita don nuni ga abin da babu tabbacin faruwarsa, ma'ana abin da yake kila wakala.
Ga misalan da suke dauke dasu kamar haka:
1. I can go around 10 o'clock (Zan iya tafiya wajen karfe goma)
2. He can come at anytime (Zai iya zuwa a kowanne lokaci)
3. She can finish today (Zata iya gamawa a yau)
4. They can be at the wedding ceremony (Zasu iya zuwa wajen bikin)
5. We can go home tomorrow (Zamu iya tafiya gida gobe)
6. I may pay the money (Zan iya biyan kudin) 
7. He may buy the ticket (Zai iya siyan tikitin)
8. She may cook for us (Zata iya yi mana girki)
9. They may finish the work (zasu iya kammala aikin)
10. We may leave before them (Zamu iya tafiya kafin su)
11. I might go for shopping (Nakan iya tafiya siyayya)
12. He might assist us (Yakan iya taimakon mu)
13. She might be happy to see us (Takan iya yin farincikin ganin mu)
14. They might be in the class now (Sukan iya kasancewa a aji yanzu)
15. We might attend the meeting (Mukan iya halartar taron)

Domin koyon turanci cikin sauki a hausance cikin tsari mai kyau a duk inda kuke a duniya  ku tuntube mu a +2348065586555

Saturday, 9 February 2019

HOW TO MAKE A COMPULSION TO YOUR SELF OR OTHERS IN ENGLISH (Yacce mutum zai tilastawa kansa ko ya tilastawa wasu a Turanci)

Sau tari mutum ya kan tilastawa kansa ko alkawartawa kansa ko wasu wani aiki ko wani abu da ya kamata yayi ko su yi.
Munada hanyoyi da dama da ake amfani dasu wajen tilastawa a kowanne yanayi da mutum zai iya tsintar kansa wajen magana a lokacin. wayan nan yanayi dai an kasasu kashi uku a takaice, sune yanayi na aikin da ake yanzu wanda muke kiransa da PRESENT TENSE sai kuma yanayi da yake nuni da aikin da wuce wato da ake kira PAST TENSE da kuma yanayin da yake nuni da aikin da za'a aikata nan gaba wato FUTURE TENSE
       Munada hanyoyi da ake amfani dasu a kowanne yanayi da muke dasu. Ga hanyoyin kamar haka:
📌PRESENT TENSE (YANAYI NA AIKIN YANZU): A wannan yanayi mukanyi amfani da HAVE TO wajen tilastawa kai ko wasu.
       Misali:


  • I have to go to school (Ya zama lallai naje makaranta)
  • You have to finish it (Ya zama lallai ka/ki kammala)
ABIN LURA:


  1. Akan yi amfani da kalmar MUST domin tilastawa kamar yacce ake amfani da kalmar HAVE TO. Misali: I must go to school (Dole naje makaranta) You must finish it (Dole ka/ki kammala)
  2. Akan yi amfani da HAS TO idan ana magana akan aikin da wani zai aikata alhalin baya wajen da ake magana a kansa.  Misali: She has to find it (Ya zama lallai ta nemo shi [abin] )

   📌PAST TENSE (YANAYIN  DA YAKE NUNI DA AIKIN DAYA GABATA): A wajen tilastawa kai ko wani akan aikin da aka riga aka kammala shi ko ya wuce misalin aikin da akayi dazu, jiya, makon daya wuce, watan daya wuce ko shekarar data wuce. A irin wannan yanayi mukanyi amfani da HAD TO
       Misali:


  • I had to go to school yesterday (Da lallai ya kamata naje makaranta jiya)
  • You had to finish it last week (Da lallai ya kamata ka/ki kammala a makon daya gabata)
    📌FUTURE TENSE (YANAYI NA AIKIN DA ZAI GUDANA): A wajen nuni ga aikin da lallai za'a aikata nan gaba kamar gobe, jibi, mako mai zuwa, shekara mai zuwa da sauransu mukanyi amfani da WILL HAVE TO.
          Misali:
  • I will have to go to school tomorrow (Lallai ya kamata naje makaranta gobe)
  • You will have to finish it tomorrow (Lallai yakamata ka/ki kammala gobe)
Ga sauran misalansu kamar haka:
(A) IN PRESENT TENSE (A yanayin da ake maganar sa a yanzu)
1. I have to wait for you (Ya zama lallai na jira ka/ki)
2. I have to cook the food (Ya zama lallai nayi girkin)
3. I have to read my book (Ya zama lallai na karanta littafi na)
4. I have to help them (Ya zama lallai na taimakesu)
5. I have to pay the money (Ya zama lallai na biya kudin)
6. You have to complete this work (Ya zama lallai ka/ki kammala aikin nan) 
7. You have know  his name (Ya zama lallai ka/ki san sunan shi)
8. They have wait for us (Ya zama lallai su jira mu) 
9. They have to clean the place (Ya zama lallai su goge wajen)
10. She has to follow us (Ya zama lallai ta biyo mu) 
11. She has to copy it (Ya zama lallai ta kwafe shi [abin] )
12. He has repair the car (Ya zama dole ya gyara motar)
13. He has to go him (Ya zama lallai  yabi shi)
14. We have to go to the market (Ya zama lallai mu tafi kasuwa)
15. We have to go now (Ya zama lallai mu tafi yanzu)
16. I must let them know (Dole na bari su sani)
17. You must sweep the room (Dole ka/ki share dakin)
18. He must go to travel to Dubai (Dole yayi tafiya zuwa Dubai)
19. They must beat him (Dole su zane shi)
20. We must help our selves (Dole mu taimaki kanmu)

(B) IN PAST TENSE (A yanayi na aikin da ya gudana a baya)
1. I had to go to the hospital (Da lallai ya kamata naje asibiti)
2. I had to let them know (Da lallai ya kamata na barsu su sani)
3. He had to call them yesterday (Da lallai yakamata ya kirasu jiya)
4. She had to finish last night (Da lallai ya kamata ta gama daren jiya)
5. We had to send him yesterday (Da lallai yakamata mu turashi jiya)

(C) IN FUTURE TENSE (A yanayi na aikin da zai wakana a gaba)
1. I will have to marry Amina (Lallai kamata na auri Amina)
2. I will have to comply with them (Lallai yakamata na yarda da yacce suke so)
3. She will have to cook for us (Lallai yakamata tayi mana girki)
4. We will have to find out (Lallai yakamata mu gano dalilin)
5. They will have to come with us (Lallai yakamata su taho tare damu)

Domin koyon turanci cikin sauki a hausance cikin tsari mai kyau a duk inda kuke a duniya  ku tuntube mu a +2348065586555

Friday, 8 February 2019

HOW TO GIVE THE ADVICE (Yacce mutum zai bada shawarar)




Har ila yau, akan yi amfani da kalmar  SHOULD don bada shawarada aka nema a turance. Wato kamar yacce akanyi amfani da kalmar wajen neman shawara to haka ake amfani da kalmar wajen bada shawarar.

  
          Ga yacce misalin amsar tambayar da akayi ta neman shawara a baya zai kasance:


  1. You should do it (ka/kya iya aikawa) 
  2. You should do the work (za ka/ki iya yin aiki) 
  3. You should buy it (ka/kya iya siyo shi) 
  4. You should assist him (ka/kya iya taimakon shi)
  5. You should respect him (ka/kya iya bashi girma)
  6. You should not wear this (kada ka/ki saka wannan)
  7. You should not stop the car (kada ka/ki tsaida motar)
  8. You should advertise your product (ka/kya iya tallata hajar ka/ki)
  9. You should visit your mother (ka/kya iya kai ziyara wajen mahaifiyar ka/ki)
  10. You should send it now (ka/kya iya aikawa yanzu)
  11. You should not follow them (kada ka/ki busu)
  12. We should not wait for them (kada mu jira su)
  13. We should work for them (ma iya yi musu aikin)
  14. They should not join us (kada su hade damu)
  15. They should go to school tomorrow (sa iya zuwa makarantar gobe) 

Domin koyon turanci cikin sauki a hausance cikin tsari mai kyau a duk inda kuke a duniya  ku tuntube mu a +2348065586555

Thursday, 7 February 2019

HOW TO ASK FOR AN ADVICE IN ENGLISH (YACCE AKE NEMAN SHAWARA A TURANCI)



A kanyi amfani da kalmar SHOULD don neman shawara a kowanne yanayi na mu'amala a harshen Turanci.
      Misalai, akanyi amfani da kalmar a tsakanin abokai ko kawaye, yan'uwa, dangi, a hukumance ko magana da wanda ya girme ka/ki ko wanda mutum ya girma.
    
       Ga misalan yacce ake amfani da kalmar a jumlace. 

  1. Should I do it? (na iya aikatawa?)
  2. Should I do the work? (na iya yin aikin?)
  3. Should I buy it? (na iya siyo shi?)
  4. Should I assist him? (na iya taimakon shi?) 
  5. Should I respect him? (na iya girmama shi?)
  6. Should I wear this? (na iya sanya wannan?)
  7. Should I  stop the car? (na iya tsayar da motar kuwa?)
  8. Should I advertise my product? (na iya tallata haja ta?) 
  9. Should I visit my mother? (na iya kai ziyara gurin mahaifiyata?)
  10. Should I send it now? (na iya aikawa yanzu?) 
  11. Should he follow them? (zai iya binsu?)
  12. Should we wait for him? (zamu iya jiran shi?) 
  13. Should we work for them? (zamu iya yi musu aiki?)
  14. Should they join us? (zasu iya hadewa da mu?) 
  15. Should they go to school tomorrow? (zasu iya tafiya makaranta gobe?)

Domin koyon turanci cikin sauki a hausance cikin tsari mai kyau a duk inda kuke a duniya  ku tuntube mu a +2348065586555

Wednesday, 6 February 2019

MAKING AN INFORMAL REQUEST AND PERMISSIONS (Use of LET/Amfani da kalmar LET)







  • LET

Ana amfani da kalmar "LET" don neman biyan bukata ko neman izini a turance a yanayin da ake kira (Informal)  wato a yanayin da mutum  zai yi magana da wayanda ya sani ko kuma shaku sosai kamar abokai/ kawaye, 'yan uwa da dangi.
        
   Ga misalan kalmar a aikace:
  1. Let me go (Bari na tafi)
  2. Let me eat (Bari na ci) 
  3. Let me speak (Bari nayi magana) 
  4. Let me see (Bari na gani)
  5. Let me drink it (Bari na sha shi) 
  6. Let him go out (Bari ya kira) 
  7. Let him do the work (Bari yayi akin) 
  8. Let her finish it (Bari ta Gama) 
  9. Let her buy it (Bari ta siya)
  10. Let them go out (Bari su fita)
  11. Let them go to school (Bari su tafi makaranta) 
  12. Let us go shopping (Bari mu tafi siyayya) 
  13. Let us have lunch (Bari muci abincin Rana) 
  14. Let us eat something (Bari muci wani abu)
  15. Let us leave now (Bari mu tafi yanzu)


Domin koyon turanci cikin sauki a hausance cikin tsari mai kyau a duk inda kuke a duniya  ku tuntube mu a +2348065586555

Saturday, 2 February 2019

MAKING FORMAL REQUEST AND PERMISSIONS (Use of Would /Amfani da kalmar Would)



  • WOULD

Would itama kalma ce da ake amfani da ita don neman izini ko wata bukata a turance kamar sauran yan'uwanta. Sai dai sau tari akan yi amfani da kalmar don bawa wanda ka/ki ke magana da shi cikakkiyar girmamawa. Haka kuma, kalmar Would  a

sau tari akan yi amfani da ita tare da kalmar "Please" don nuna cikakkayar girmamawa don neman biyan bukata a take. Misali: Would you please assist me? (Zan iya samun taimakon ka/ki kuwa?) 

     Ga misalai da kalmar Would kamar haka:

  1. Would you please wait for me? (za ka/ki iya jirana kuwa?) 
  2. Would you please read it for me ? (za ka/ki iya karantamun shi (abun/rubutun) kuwa?)
  3. Would you give this letter to her? (za ka/ki iya bata wasika/sako na kuwa?)
  4. Would you please hold it for me? (za ka/ki iya rike min kuwa?) 
  5. Would I take tomorrow off ? (za iya daukar hutu gobe?)
  6. Would I stay here for two days? (zan iya zama anan na tsahon kwana biyu) 
  7. Would I use your laptop? (zan iya amfani da komfiyutar ka ta tafi da gidanka?)
  8. Would I see this book please? (zan iya ganin littafin nan kuwa?)
  9. Would you please repeat it please? (za ka/ki iya maimaitawa kuwa?) 
  10. Would you keep the money for me? (za ka/ki iya ajiye min kudin?)


Thursday, 31 January 2019

MAKING FORMAL REQUEST AND PERMISSION (Use of Could/Amfani da Could don neman biyan bukata ko kuma izini)

  •  Could
Hanya ta Uku da ake amfani da ita wajen neman biyan bukata ko kuma izini ita ce hanyar
amfani da kalmar Could. Ana amfani da ita ne sosai a hukumance ko wajen magana da wanda ya girme ka/ki. Amfi so ayi amfani da ita don nuna cikakkiyar girmamawa ga wanda ake magana da shi.
  
        Ga misalan inda zakuyi amfani da ita kamar haka:
  1. Could I make a call? (shin wai zan iya yin kira?)
  2. Could you please open the door? (shin wai za ka/ki iya bude kofar?)
  3. Could you turn down the music? (shin wai za ka/ki iya rage sautin kidan?)
  4. Could you tell me what time it is? (shin wai za ka/ki iya gayamin lokaci?)
  5. Could I take one? (shin wai zan iya daukar guda/daya?)
  6. Could I ask a question? (shin wai zan iya tambaya?)
  7. Could we go home now? (shin wai zamu iya tafiya gida yanzu?)
  8. Could you take the message please? (shin wai za ka/ki iya karbar sakon?)
  9. Could you carry this for me? (shin wai za ka/ki iya daukar min wannan[abu]?)
  10. Could I pay the money for the goods? (shin wai zan iya biyan kudin kayan?)

Wednesday, 30 January 2019

MAKING A FORMAL REQUEST AND PERMISSIONS (Use of May/ Amfani da kalmar May)

  • May
 May Itama kalma ce da ake amfani da ita wajen neman izini kamar yadda ake amfani da Can har ma sau tari akan fi amfani da ita don neman izini wajen wanda ya girme ka/ki fiye da yar uwarta Can.

     Ga misalai da kalmar May kamar haka:

  1. May I see it? (shin zan iya ganin sa [abu]?)
  2. May I wait for you? (shin zan iya jiran ka/ki?)
  3. May I wait here? (shin zan iya jira anan?)
  4. May I sit with you? (shin zan iya zama tare da kai/ke?)
  5. May I invite him? (shin zan iya gayyatar sa?)
  6. May I bring it? (shin zan iya kawo shi [abu]?)
  7. May I take it? (shin zan iya daukar sa [abu]?)
  8. May I buy the food? (shin zan iya sayo abinci?)
  9. May I go to the bank? (shin zan iya zuwa banki)
  10. May I go to the hospital? (shin zan iya zuwa asibiti?)
  11. May I go to his house? (shin zan iya zuwa gidanshi?)
  12. May I go to the event? (shin zan iya zuwa taron?)
  13. May I come in? (shin zan iya shigowa ciki?)
  14. May I know your name? (shin zan iya sanin sunan ka/ki?)
  15. May I accompany you? (shin zan iya raka ka/ki)

Tuesday, 29 January 2019